Ministar harkokin mata, Hajiya Aishatu Isma'ila ta soma yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar yakin neman zabe na shekarar 2019. Ministar, wacce ta jagoranci shugabannin jam'iyyar APC na jihar Taraba domin kai gaisuwar Sallah ga Atiku Abubakar, ta yi addu'ar Allah ya ba shi shugabancin kasar a 2019.
Wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian wacce ake wallafawa a shafin intanet ta buga, ya nuna ministar a gaban tsohon mataimakin shugaban kasar tana cewa, "Your Excellency (mai girma), babanmu, shugaban kasarmu idan Allah ya yarda a shekarar 2019... a gabanka, mutanenka ne, magoya bayanka har abada; mutanen jihar Taraba.
"Sun zo gaisuwar ban-girma, gaisuwar Sallah da kuma yi maka murna ta wannan daukaka (Wazirin Adamawa) da Allah ya kara Minista Alhassan ya gabatarwa tsohon mataimakin shugaban kasar shugabannin jam'iyyar, tana mai cewa wasunsu sun matsa domin su yi jawabi a gabansa amma hakan ba zai yiwu ba saboda ya gaji.
Tawagar ta rika yin tafi a lokacin da ministar ke wadannan jawabai.
Ministar ta harkokin mata dai ita ce ta yi takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam'iyyar APC a shekarar 2015, ko da yake ta sha kaye a hannun Gwamna mai-ci, Darius Ishaku na jam'iyyar PDP.