Jarumin fina finan nan Hausa Adam A Zango ya ce lafiyarsa kalau sabanin jita-jitar da ake yadawa cewa an yi mi shi duka.
Jarumin ya karyata jita-jitar da ake yadawa a dandalin sada zumunta na intanet a inda ake yada labarin cewa barayi sun jikkata shi a sakamakon dukan da suka yi masa.
Shahararren mawakin ya kara da cewa hotunan da ake yadawa da raunuka a jikinsa na fim din Basaja ne wanda ake yi masa kwalliya, ba raunin gaske ba ne. Ya kuma yi kira ga masu kirkirar irin wadannan karai rayi da su daina.